Bangaren kasa da kasa, Jaridar The Guardian da ake bugawa a kasar Birtaniya, ta buga wani rahoto da ta harhada dangane da da yakin da Saudiyya take kaddamarwa a kan al'ummar kasar Yemen a fitowarta ta jiya Alhamis.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya
habarta cewa,
A cikin rahoton nata, jaridar ta ce kisan kiyashin da ake
yi wa al'ummar kasar Yemen ba aikin kasar Saudiyyah ne ita kadai ba, tana yin
hakan ne tare da gwamnatin Birtaniya, domin Birtaniya ce ke sayar wa Saudiyya
da mafi yawan makaman da take yin amfani da su wajen aki hare-hare a kan
biranan Yemen, da suka hada har da makaman cluster da aka haramta yin amfani da
su a duniya.
Jaridar ta ce bai kamata a rufe ido saboda
maslaha ta ribar makamai da ake samu a yakin Yemen ba, domin kuwa abin da
ake yi kisan fararen hula ne, wanda yake a matsayin laifin yaki, kuma lokaci na
zuwa da dukkanin abin da ake yi kullawaa asirce zai bayyana ga kowa a duniya.
3555937