Kamfanin dilalncin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Ahlu tafsir cewa, gudanar da taron kan mujizar kur’ani mai tsarki karo na biyar a birnin Zakazik na jahar Sharqiyyah a kasar Masar.
Wannan taro dai zai samu halartar masana daga kasashen duniya musamman na musulmi da na larabawa, inda za a duba wasu lamurra masu matukar muhimamnci danganea da matsayin kur’ani mai sarki ta fuskar balaga da sauransu, da ke tabbatar da mujizar wannan littafi mai tsarki.
Abubuwa kamar guda 5 da za a yi dubi kansu suna hada da:
1 – Mujizar kur’ani ta fuskar balaga: kur’ani mai tsarki ba shi da kwatankwaci fuskar balaga da tsari na Magana ta hikima.
2 – Mujizar kur’ani ta fuskar adabi da salo: wanda hakan ya hada da yadda kur’ani ke bayar da kissoshi a cikin tsari da ba a san da su ba, labarin kiyama, da kuma yadda yake ambatar adadi.
3 – Mujiza ta fuskar lugga: kur’ani yana amfani da lafuzza na balaga wanda masu ilimi a wannan bangare za su fi saurin gane hakan.
4 – Mujiza ta fuskar ilimi: kur’ani yana tattare da ilmomi a dukkanin bangarori na sanin yanayi, zamatakewa, ilimin taurari, halayen dan adam da sauransu.
5 – Mujiza ta fuskar tarihi: ku’ani mai tsarki ya kawo bayanai na tarihi tabbatace dangane da al’ummomin da suka gabata, da hakan ya hada da labarin annabawa da jamarsu, da kuma yake-yaken da aka yi a zamnin da.
6 – Mujiza ta fuskar harshe: kur’ani mai tsarki ya yi ishara da matsayin harsuna da matsayinsu a cikin al’umma da tasirinsu, inda hatta kalmomin da ake amfani da su sun hada da wasu yarukan ba larbaci ne kawai a cikin kur’ani, amma kur’ani ya larabtar da su.
7 – Mujiza ta fsukar shari’a: kur’ani ya kasance littafi daya kunshi rsari na shari’a da kare hakkin bil adama, da kuma adalci.