IQNA

Trump Ba Zai Iya Aiwatar da Shirinsa Na Korar Musulmi Daga Amurka Ba

22:39 - December 24, 2016
Lambar Labari: 3481065
Bangaren kasa da kasa, Dave Lindorff fitaccen marubuci dan kasar Amurka ya bayyana cewa, Trump ba zai iya aiwatar da shirinsa na korar musulmi ko hana su shiga Amurka ba.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, a lokacin zantawarsa da tashar Press TV marubucin ya bayyana cewa, a lokacin yakin neman zabe Trump ya yi kalamai da daman a shirin da yake da shi na hana musulmi shiga Amurka, amma a halin yanzu hakan ba zai yiwu ba.

Kamfanin dillancin labaran Politici ya habarta cewa,a lokacin da yake amsa tambayoyin manma labarai a jiya, dangane da abin da ya far u na kai harin birnin Berlin na jamus Trump ya bayyana cewa, hakika abin da ya faru aiki ne na ta’addanci.

Da aka tambaye shi ko har yanzu yana nan kan bakansa na hana musulmi shiga cikin kasar Amurka bisa alkawalin da ya yi idan har ya ci zabe, sai ya ce; akwai musulmi sama da biliyan daya da iliyan dari shida a duniya, babu yadda za a yi mutum ya shiga takun saka da su baki daya.

Dan jaridar ya ce dukkanin kalaman da Trump ya yi na barazanar korar musulmi ko hana su shiga cikin Amurka Magana ce ta yakin neman zabe, domin da hakan ne kawai zai iya faranta ma wasu, musamman masu kyamar musulmi, kuma zai samu kuri’arsu.

Kamar yadda ya yi amfani da batun ta’addanci tare da jingina hakan ga Hillary Cliton da ta yi takara da shi, domin ya bakanta sonata aidon Amurkawa, kasanutuwar tana da alaka wajen kafa kungiyoyin ‘yan ta’adda, kamar yadda kuma aka tabbatar da hakan ta hanyar wasu kalamanta da kuma wasikun da ta rika aikewa da yanar gizo tsakanita da wasu mutane.

3556175


captcha