IQNA

Daya Daga Cikin Wadanda Ake Zargi Da Kai Harin Alkahira Ya Shiga Hannu

23:50 - January 06, 2017
Lambar Labari: 3481108
Bangaren kasa da kasa, Jami'an tsaron kasar Masar sun cafke daya daga cikin mutanen da ake zargi da hannu a harin da aka kai kan majami'ar mabiya addinin kirista a birnin Alkahira.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga tashar alalam cewa, A cikin wani bayani da ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Masar ta fitar a yammacin jiya ta sanar da cewa, an samu nasarar cafke Karam Ahmad abdul Al, daya daga cikin mutanen da ake zargi da hannu a harin da aka kaddamar kan majami'ar birnin Alkahira.

Bayanin ya ce an samu makamai da kuma wasu ababuwa masu fashewa da sanadaran hada bama-bamaia wurin da aka damke shi, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarinsa.

A cikin watan Disamban da ya gabata ne dai aka kaddamar da harin bama-bamai a kan babbar majami'ar mabiya addinin kirista abirnin Alkahira na kasar Masar, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 28, tare da jikkatar wasu da dama, kungiyar ISIS ta dauki alhakin kaddamar da harin.

3559892


captcha