IQNA

An Bude Sabon Babban Masallacin Birnin Khartum

19:45 - January 07, 2017
Lambar Labari: 3481111
Bangaren kasa da kasa, an bude sabon babban masallacin birnin Khartum fadar mulkin kasar Sudan a unguwar Alazhari da ke birnin.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na smc.sd cewa, an gudanar da tarun bude masallacin ne wanda cibiyar ayyukan alkhari ta UAE ta gina tare da halartar jami’a da kuma al’ummar gari.

Muhammad hamad Aljunaibi jakadan kasar IAE a Sudan ya gabatar da jawabi a wurin, inda ya ce hakika wannan masallaci yana daga cikin muhimman ayyukan da wannan cibiya ta gudanar a kasar Sudan, duk kuwa da cewa ya zuwa ta gina masallatai sun kai kimanin 300 a kasashen duniya.

Ya ce manufar gina wannan babban masallaci ita ce yada koyarwa irin ta addini da kuma tunatarwa gami da jawo hankalin matasa musulmi, dangane da bin sahihiyar koyarwa irin ta kur’ani, maimakon shiga kungiyoyin masu tsatsauran ra’ayi da ke wuce gona da iri a cikin lamarin addini.

Jabir Idris Awisha shugaban kwamitin kula da harkokin wa’azi na kasar Sudan, wanda shi ma ya gabatar da nasa jawabin a wurin ya bayyana cewa, wajibi ne matasa musulmi su tunkari irin kalu balen da ke a gabansu a wanann zamani, ta hanyar sanin hakikanin addini, domin kuwa su ne suka fi saukin bin hanyoyi na rudu, inda akan wanke musu tunani da sunan addini,ko kuma su shiga cikin masu sha kwayoyi.

Daga karshe ya yaba wa wannan cibiya da ke gudanar da ayyuka na alkhari ta Fajr, tare da yin fatan al’ummar Sudan su gajiyar ayyukan da take gudanawa, da hakan ya hada da gina masallatai 28 yanzu a larduna daban-daban na kasar.

3560201


captcha