IQNA

19:48 - January 07, 2017
Lambar Labari: 3481112
Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Masar ya ce za a gidana babban masallaci da kuma babbar majami’a a sabon babban birnin kasar da za a gina.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Ahram cewa, a ranar Juma’a da ta gabata shugaban kasar Masar Abdulfattah Sisi ya ziyarci babbar majami’ar birnin Alkahira ta mabiya addinin kirista Kibdawa, wadda aka kaiwa hari a kwanakin baya.

A lokacin rangadin shgaba Sisi ya bayyana cewa, daya daga cikin tsarin da suke da shi a halin yanzu shi ne za a gina masallaci mafi a kasar Masar da kuma majami’a mafi girma a kasar a sabon babban birnin kasar da za a gina.

Ya ce mabiya addinin muslunci da kiristoci ‘yan kasar Masar dukkaninsu ‘yan kasa ne, babu wani wanda zai iya cirewa wani daga cikin rigar izinin zama dan kasa, a kan haka gwamnatinsa ba za ta bari wasu masu akidar ta’addanci su kawo rashin jitwa a tsakanin al’ummar Masar da sunan addini ba.

Za a gina sabon babban birnin Masar ne kilo mita 45 a gabashin birnin Alkahira, babban birnin kasar na yanzu, inda dukkanin manyan ma’aikatun gwamnati da ofisoshin jakadancin kasashen ketare za su koma wurin.

3560183


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: