Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Ahram cewa, a ranar Juma’a da ta gabata shugaban kasar Masar Abdulfattah Sisi ya ziyarci babbar majami’ar birnin Alkahira ta mabiya addinin kirista Kibdawa, wadda aka kaiwa hari a kwanakin baya.
A lokacin rangadin shgaba Sisi ya bayyana cewa, daya daga cikin tsarin da suke da shi a halin yanzu shi ne za a gina masallaci mafi a kasar Masar da kuma majami’a mafi girma a kasar a sabon babban birnin kasar da za a gina.
Ya ce mabiya addinin muslunci da kiristoci ‘yan kasar Masar dukkaninsu ‘yan kasa ne, babu wani wanda zai iya cirewa wani daga cikin rigar izinin zama dan kasa, a kan haka gwamnatinsa ba za ta bari wasu masu akidar ta’addanci su kawo rashin jitwa a tsakanin al’ummar Masar da sunan addini ba.
Za a gina sabon babban birnin Masar ne kilo mita 45 a gabashin birnin Alkahira, babban birnin kasar na yanzu, inda dukkanin manyan ma’aikatun gwamnati da ofisoshin jakadancin kasashen ketare za su koma wurin.