IQNA

23:46 - January 08, 2017
Lambar Labari: 3481115
Bangaren kasa da kasa, sakamakon matsin lamba da sha kakkausar ska gwamnatin Myanmar ta amince a warware matsalar musulmin kasar ta hanyar diflomasiyya.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Iina cewa, gwamnatin Myanmar ta sanar da cewa za ta aike da wata tawaga zuwa kasar Bangaladash domin duba halin da ‘yan kasar masu gudun hijira suke ciki a sansanonin da aka tsugunnar da su.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Bangaladash ta ce, tawagar za ta tattauna batnun ‘yan kabilar Rohingya ne da suka yi gudun hijira zuwa Bangaladash ne kawai ta da hukumomin kasar, domin bin matakai na diflomasiyya wajen warware matsalarsu.

Tun a cikin watan Nuwamban shekarar da ta gabata ce dai jami’an sojin kasar Myanmar da kuma wasu ‘yan addini Buda masu tsatsauran ra’ayi, suka afka kan musulmi a kasar ta mayanmar, ida suka kasha adadi mai yawa da cikinsu, tare da yi ma matansu fyade, da kuma rusa musu gidaje tare da kone musu dokiyoyi da kaddarori.

Wannan mummunan aiki ya fuskanci kakausar suka daga kasashen duniya musamman ma ‘yancin siyasa daga cikinsu, gami da wasu daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa, kamar yadda a ranar Juma’a da ta gabata, kasar Iran ta bukaci majalisar dinkin duniya da ta sanya baki kan kisan gillar da ake yi wa musulmi a Myanmar, inda a jiya MDD ta sanar da cewa za ta binciki wannan lamari da gaske.

3560589


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: