IQNA

23:15 - January 09, 2017
Lambar Labari: 3481118
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki karo na 31 a Najeriya wadda za a ci gaba da gudanar da ita har tsawon mako guda.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya bayar da rahoton cewa ya nakalto daga shafin yanar gizo na jaridar Daily Star cewa, Muhammad Abdullahi Aubakar gwamnan jahar Bauchi da yake halartar wajen taron bude gasar, ya jaddada muhimmancin yin aiki da koyarwar kur’ani.

Inda ya ce nauyi ne akan kowane musulmi ya yi da koyarwar kur’ani mai tsarki, domin kuwa kur’ani yana a matsayin littafin dokoki ne ga dukkanin musulmi, wanda shi ne jagoransu wajen birnin umarnin Allah madaukakin sarki.

Gwamnan ya kara da cewa, gwamnatinsa za ta kara zage dantse wajen ganin ta kara bunkasa ayyukan kur’ani a jahar, kamar yadda kuma za ta ci gaba da daukar nauyin dalibai da suke wakiltar jahar zuwa gasa a dukkanin jahohin kasar.

Baba Madugu wanda shi ne shugaban kwamitin kula da harkokin addini a jahar Bauchi, ya bayyana a wajen taron cewa, yau kimanin shekaru talatin da daya kenan ana gudanar da gasar karat da hardar kur’ani a cikin jahohi 20 na kasar.

A cewarsa wannan babbar nasara ce ga dukkanin musulmi a kasar, kumaa wannan karo taron gasar yana gudana a jahar Bauchi, wanda kuma hakan yana kara karfafa giwar matasa waje ganin sun mayar da hankali ga lamarin kur’ani.

Ansa bangaren Dr. Zubair Abubakar Madaki ya bayyana cewa, akwai kimanin makaranta da mahardata 220 da suka hada da maza da mata da ke halartar wannan asa.

3561319


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: