IQNA

21:22 - January 10, 2017
Lambar Labari: 3481121
Bangaren kasa da kasa, kafofin yada labarai da daman a kasashen ketare sun nuna taron janazar Ayatollah Hashimi Rafsanjani a yau kai tsaye.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, dubban gomomin al’umma ne suka halarci janazar Ayatollah Hashimi Rafsanjani a yau.

Tashar talabijin ta kamfanin dillancin labaran Associated Press APTN ta bayar da rahoto kai tsaye daga birnin Tehran a lokacin da ake gudanar da janazar shugaban majalisar fayyace maslahar tsarin muslunci Ayatollah Hashimi Rafsanjani.

Tashoshin Almayadeen, Aljazeera, Mubashir, France24, Aljazeera English, BBC, EURO News, sun nuna wani bangare na janazar kai tsaye a lokacin da ake gudanar da ita.

Abin tuni a nan dai shi ne, taron janazar marigayi Ayatollah Hashimi Rafsanjani, ya samu halartar jami’ai daga kasashen ketare, da suka hada da ministan harkokin wajen kasar Iraki Ibrahim Jafari, da kuma Ammar Hakim.

3561481


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: