IQNA

Karbar Izini Daga Azhar Sharadin Halartar Madaba’antun Masar A Baje Kolin Turkiya

23:02 - January 12, 2017
Lambar Labari: 3481126
Bangaren kasa da kasa, shugaban hadakar madabantun kasar Masar ya bayyana cewa, sharadin kai littafan Masar a baje kolin da za ayi a Turkiya shi ne karbar izini daga Azhar.

Kamfanin dilalncin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga jaridar Yaum Sabi cewa, Adel Almisri shugaban hadakar madabantun kasar Masar ya tabbatar da cewa karbar izini daga Azhar shi ne sharadin kai littafan Masar a baje kolin da yi a Turkiya.

Ya ci gaba da cewa, an riga a sanar da dukkanin madaba’antu da suke buga littafai a kasar musamman ma masu buga littafai da suka shafi kur’ani kan cewa dole nea nemi izini a rubuce daga Azhar kafin a kai wasu littafai a wannan baje koli.

Haka nan kuma akwai sharuddan da aka gindaya dangane da irin littfana da za s bsje, dole ne su zama littafai na ilimi wadanda aka buga su a madabantun, kuma ba a yarda a kai wasu littafai daddau da suke amatsin na tarihi ba.

Ya kara da cewa har yanzu babu wani littafi da aka hana wucewarsa daga cikin jerin littafan da madaba’antu da dama suka nemi zini a kansu daga cibiya ta Azhar.

A cikin wata mai kamawa ne dai za agudanar da bababn baje kolin littafai na kasa da kasa a birnin Istanbul na kasar Turkiya, wanda zai samu halartar daruruwan madabantu daga kasashen ketare.

3561802


captcha