IQNA

Masarautar Bahrain Na Ci Gaba Da Hana Sallar Juma'a A Unguwar Diraz

20:40 - January 13, 2017
Lambar Labari: 3481129
Bangaren kasa da kasa, masarautar kasar Bahrain na ci gaba da hana gudanar da sallar Juma'a a unguwar Diraz da ke kusa da birnin Manama fadar mulkin kasar.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Mir'at Manama cewa, jami'an tsaron masarautar Bahrain sun killace dukkanin yankuna da hanyoyin da ke isa masallacin Imam sadiq (AS) babban masallacin Diraz domin hana gudanar da sallar Juma'a a yau.

Bayanin ya ce wannan mataki ya zo ne tun fiye da watanni shida da suka gabata, bayan da masarautar mulkin kama karya ta kasar Bahrain ta sanar da janye izinin zama dan kasa daga kan babban malamin addinin muslunci na kasar Ayatollah Sheikh Isa Kasim.

Wasu wadanda suka ganewa idanunsu sun ce jami'an tsaron masarautar Bahrain sun kame wasu daga cikin musulmi da suke niyyar tafiya zuwa masallacin Juma'a na Imam Sadiq (AS) da ke yankin na Diraz domin gudanar da sallar Juma'a, kamar yadda kuma suka hana limamin masallacin Isa wurin.

Fiye da watanni 6 kenan a jere masarautar mulkin kama karya ta Bahrain tana hana musulmi yin sallar Juma'a wannan masallaci, tare da killace al'umma da kuma hana su zuwa wurin.

3562208



captcha