BKamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga tashar alalam cewa, shugaban cibyar bunkasa al'adu ta kasar Iran ya sheda cewa, za agudanar da wannan taro ne tare da halartar masana 85 daga kasashen larabawa 12, wanda za a fara a Tehran, kuma za a kammala shi a birnin Mashhhad
Abu Zar Ibrahim Turkumani ya kara da cewa, wannan taro zai mayar da hankali ne kan muhimamn batutuwa da suka danganci matasa, da kuma yadda za a kara bunkasa alaka ta al'adu da koyar muslucni a tsakanin matasan kasashen.
Za a gudanar da tarukan ne a jami'oin Allamah Tabatab'i da kuma jami'oin Zahra