Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, tashar PressTV ta bayar da rahoton cewa, mai rikon mukamin babban daraktan kungiyar ta Amnesty International a NijeriyaMakmid Kamara ne ya yi wannan kiran inda ya ce a yau Litinin ne wa'adin kwanaki 45 da babban kotun ta Abuja ta ba wa gwamnatin Tarayyar kasar da ta sake Sheikh El-Zakzaky din yake cika, don haka ya zama wajibi ne gwamnatin ta sake shi, in kuwa ba haka ba, to hakan yana a matsayin yin karen tsaye ne ga doka.
Har ila yau kuma kungiyar Amnesty International din ta bukaci gwamnatin da ta saki saura 'yan kungiyar Harkar Musulunci din (IMN) da su ma aka kama su tare da shugaban na su kuma ake ci gaba da tsare su.
A ranar 2 ga watan Disambar bara (2016) ne alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja mai shari'a Gabriel Kolawole ya bukaci gwamnatin da sake Sheikh El-Zakzaky da matarsa Zeenat Ibrahim cikin kwanaki 45 da kuma biyansu diyyar Naira miliyan 50 saboda tsare su da aka yi ba tare da shari'a ba.
A watan Disamban shekara ta 2015 ne jami'an tsaron Nijeriya suka kama Sheikh El-Zakzaky a gidansa da ke Zariya bayan wani rikici da ya shiga tsakanin mabiyansa da sojojin Nijeriya a garin na Zaria, inda aka kashe daruruwa daga cikin mabiyan nasa.