IQNA

Gasar Harda Da Karatun Kur'ani Ta Duniyar Musulmi Karo Na Biyu Ta Masu Nakasa

17:47 - January 20, 2017
Lambar Labari: 3481151
Bangaren kasa da kasa, cibiyar da ke daukar nauyin shirya gasar kur’ani ta kasar Iran za ta shirya gudanar da gasar harda da karatun kur’ani mai tsarki ta nakasassu daga kasashen musulmi.

BKamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, wannan gasa ta shafi maza ne zalla, kuma lokacin gudanar da gasar shi ne kamar haka: 19 zuwa 26 ga watan Afirilu 2017.

Ga bayani danganeda gasar ga wadanda suke son su halarta

Bangarorin gasar:

- Hardar dukkanin kur'ani mai tsarki

- Karatun kur'ani mai tsarki

Sharuddan wanda zai halarci gasar:

1 – Zama cikakken dan kasa daga kasar da mutum zai zo

2 – Wanda zai halarta, ya zama bai halarci gasar da aka gudanar a shekarar da ta gabata a kasar Iran ba

3 – Ya zama yana iya yin karatun kur'ani tare da kiyaye dukkanin ka'idoji da hukunce-hukunce na tajwidi da kyakkyawan sauti

4 – Wanda zai halarta, bangare daya ne kawai na gasar zai iya shiga

5 – Daga kowace kasa mutum daya ne kawai zai iya raka masu shiga gasar

6 – Daukar nauyin VISA, tikitin jirgi da mutum guda dan rakiya, da wurin zama, duk yana kan cibiyar shirya gasar kur’ani

7 – Abubuwan da ake bukata:

Shafin farko na Passpot da ke dauke da hoto da bayanin mutum, kananan hotuna guda 2, tare da form din rijista da mutum ya cika

8 – Wa’adin karshe na karbar wadannan abubuwa:

15 ga Bahman shekara 1395 Shamsiyya, 5 Jumada ula 1438 HJ, wanda ya yi daidai da 3 ga Fabrairun 2017.

9 – Za a iya ziyartar wannan shafi na cibiyar da ke daukar nauyin shirya wannan gasa: www.quraniran.ir

Haka nan kuma za a iya tuntubar wadannan lambobin waya domin neman Karin bayani:

- Wayar salula : 0098 922 3784093

- Layin kasa da Fax: 0098 2164872627

- Adireshin email: awqafiran@yahoo.com

- Hanyar tuntuba ta Telegram da WhatsApp da hanyoyin sada zumunta: 0098 9223784094.

3461961


captcha