IQNA

Wasu Daga Cikin jaridun Birtaniya Sun Gyara Kurasu kan Musulmi

23:54 - January 21, 2017
Lambar Labari: 3481157
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin jaridun kasar Birtaniya sun gyara kuran da suke suke na rubuta labaran karya akan musulmin kasar.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani an IQNA ya habarta cewa, jaridar Mail Online ta habarta cewa, sakamakon buga wasu labarai marassa tushe da ta yi kan musulmi, ya zama tilasta akanta ta sake dawowa ta gyara kuren da ta yi.

A cikin kwanakin bayan nan dai kimanin labarai 20 nea aka buga a manyan jaridun kasar Birtaniya a kan msuulmi wadanda bas u da tushe balantana makama, wanda aka tilast su suka goge labaran kuma suka nemi uzuri daga musulmi da kuma masu karatu.

A nata bagaren cibiyar da ke kula da harkokin msuulmi a akasar ta Birtaniya ta bayayna cewa, tana bin kadun dukaknin abin da jaridun kasar suke bugawa akan msuulmi,a akan haka ne ma ta talista jaridun da suka bayar da rahotonnin karya suka canja rahotannin nasu.

Bayanin y ace daga cikin jaridun jaridar The Sun, sai kuma jaridar Express gami da jaridar Mai Online, wadanda suka buga labarai daga bisani kuma ta bayyana cewa karya ce aka danganta ga musulmi.

Cibiyar ta kara da cewa, irin wadannan rahotanni su ne suke kara tunzura masu kyamar musulunci daukar matakin cin zarafin msuulmi a kasar da kai hari a wuraren ibada da kuma masalatai.

3564956


captcha