IQNA

Kwamitin Malaman Musulmi Na Duniya Ya Gargadi Trump

22:57 - January 22, 2017
Lambar Labari: 3481159
Bangaren kasa da kasa, kwamitin malaman addini na musulmi a duniya ya yi gargadi dangane da duk wani yunkuri na dauke ofoshin jakadancin Amrka daga birnin Tel aviv zuwa Quds.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Anatoly na kasar Turkiya cewa, kwamitin malaman ya fitar da bayani wanda a cikinsa ya yi gargadi kan aiwatar da wannan manufa.

A cikin bayanin an bayyana cewa, kwamitin yana yana kira ga dukkanin al’ummar musulmi ta uniya da ta tsaya kai da fata wajen ganin an kare hakkokin al’ummar Palastinu, ta hanyar bin kaidoji na doka da kuma tsari na majlaisar dinkin duniya a kan wannan batu.

Bayanin ya kara da cewa, babbar manufar yin hakan ita ce kara rauna amusulmi, tare da kuma karfafa sahyuniyawa da suke mamaye da yankunan musulmi a cikin palastinu, da hakan ya hada da wurare masu alfarma.

A kan haka kwamitin malaman ya ce babban hadarin hadarin da wannan yunkuri yake da shi a kan musulmi shi ne, ana shirin mayar da mamayar yankunansu a birnin Quds da yahudawan sahyuniya key i a matsayin halastaccen lamari a hukumance.

Abin tuni a nan dai shine, tun a cikin shekara ta 1995 ne majalisar dokokin kasar Amurka ta amince a akn dauke ofishin jakadancin Amurka daga Tel Aviv zuwa Quds, amma shugabannin Amurka da aka yi daga lokacin zuwa yanzu suka aiwatar da hakan, saboda ya sanawa maslahar Amurka ta bangarorin da dama.

3565300


captcha