IQNA

Wani Dan Malaysia Mai Larurar Shanyewar Wasu Gabbai Ya Hardace Kur’ani

22:27 - February 13, 2017
Lambar Labari: 3481227
Bangaren kasa da kasa, wani dan kasar Malaysia mai fama da matsalar shanyewar wasu gabban jiki ya yi nasarar hardace kur’ani mia tsarki.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Malaysian Digest cewa Ahmad Zahiruddin wani dan kasar Malaysia ne mai fama da matsalar shanyewar wasu bangarorin jikinsa, wanda kuma ya samu damar hardace ku’ani mai tsarki.

Zahiriddini ya bayyana cewa, hakika hardar kur’ani mai tsarki wani babban lamari ne da ke in gagrumin tasiria cikin rayuwar mutum, domin kuwa mutum yana kara samun natsuwa da kuma zama mai hakuri a rayuwarsa.

Ya ce ya fuskanci matsaloli masu tarin yawa kafin ya hardace kur’ani, ganin irin larurar da ke tare da shi, amma da taimakon Allah da kuma taimakon mahaifinsa, Allah ya taimake shi ya hardace kur’ani baki daya.

Ahmad ya kasance dalibi ne a wata makarantar kur’ani a birnin Kualalampour, kuma ya mayar da hankali matuka ga karatunsa, wanda hakan ne ma ya kara masa karfin gwiwa domin ganin ya hardace kr’ani mai tsarkia rayuwarsa, wanda kuma Allah madaukakin sarki ya cika masa burinsa.

Labarinsa dai ya cika jaridu da kafofin yada labarai na kasar na addini da ma wadanda ban a addini ba, domin kuwa shi ne mutm na farko da ke fama da irin larurasa da ya hardace kur’ani a tarihin kasar.

3573901


captcha