IQNA

Kungiyar Amnesty Int. Ta Yi Kakkausar Suka Kan Cin Zarafin 'Yan Adam Myanmar

16:18 - February 24, 2017
Lambar Labari: 3481259
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty Int. ta yi Allawadai da kakakusar murya dangane da kisan kiyashin da aka yi wa musulmi a Myanmar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya nakalto daga shafin Arakan cewa, a cikin rahoton shekara-shekara da kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty Int. take fitarwa, shekarar bana ta bayyana kisan kiyashin da aka yi wa musulmi 'yan kabilar Rohingya a Myanmar a matsayin daya daga cikin munanan ayykan cin zarafin bil adama a wannan shekara.

Rahoton ya ce bisa ga dukkanin rahotonni da kungiyoyin kare hakkin bil adama suka tattara, da suka hada da kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya, da kuma wanda ita kanta kungiyar ta Amnesty ta harhada, dukkanin rahotani suna yin nuni da abu guda daya ne, kan kisan kiyashin da aka yi yan kabilar Rohingya.

Kungiyar ta ce ya zama a dauki dukkanin matakan ad suka dace domin ladabtar da wadanda suke da hannu cikin lamarin, da kuam gabatar da a gaban kuliya domin hukunta su, musamman ganin cewa lamarin ya hada da jami'an tsaron kasar wadanda ya kamata su kare doka da rayukan faraen hula, amma suka bage da kisan fararen hula.

Kabilar Rohingya wadanda su ne marassa a rinjaye a kasar ta Myanmar, sun fuskanci kisan gilla daga jami'an tsaro da kuma masu tsatsauran ra'ayin addinin buda a cikin shekarar da ta gabata, inda daga karshe dai wasu daga cikin kasashen yankin da kuma wasu daga cikin kasashen musulmi suka tashi domin kalubalantar wannan lamari.

3577652


captcha