IQNA

Morocco Ta Bayar Da Kyautar Kwafin Kur’ani Dubu 10 Ga Kasar Guinea

23:37 - February 25, 2017
Lambar Labari: 3481260
Bangaren kasa da kasa, sarkin Morocco Muhammad na shida a ziyarar da ya kai kasar Guinea ya bayar da kyautar kwafin kur’ani mai tsarki ga limamai malaman addini.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, shafin Almisr arabiyyah ya bhabarta cewa, Muhammad na shida nba kasar Morocco ya isa birnin Conakry fadar mulkin kasar Ginea, inda ya yi sallar Juma’a tare da shuga Alfa Konde.

Bayan kammala sallar Juma’a sarkin na Morocco ya bayar da kyautar kwafin kur’anai ga malamai da kuma limamai da wasu daga cikin jami’ai a bangaren addini na kasar.

Abdulkarim Chubati shi ne minister mai kula da harkokin addini n akasar ta Guinea, shi ne kuma ya karbi wannan kyauta.

Abin tuni a nan dai shi ne fiye da malamai 114 ‘yan kasar Guinea ne suka samu horo na addini a wani shiri da sarkin Morocco ya shirya a kasarsa, wadanda wasunsu lmamai ne a halin yanzu, wanda shirin kuma ya samu halartar wasu daga cikin kasashen Afirka.

3577837


captcha