IQNA

An Tarjama Hikimomin Nahjul Balagha A Cikin Harshen Senegal

16:44 - February 26, 2017
Lambar Labari: 3481263
angaren kasa da kasa, an tarjama hikimomin da ke cikin littafin Nahjul-balagha daga kalaman Amrul muminin (AS) a cikin harshen Wolof.

BKamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, shafin bangaren hulda da jama'a na ma'aikatar kula da harkokin ilimi da al'adun muslunci na Iran ya habarta cewa, an tarjama hikimomin kalaman Amirul muminin (AS) da ke cikin littafin nahjul balagha a cikin harshen Wolof da ake Magana da shi a Senegal.

Karamin ofishin jakadan Iran da ke kasar Senegal ne ya dauki nauyin tarjama wannan bangare na littafin Nahjul Balagha, wanda shekhuna Lauh babban mai tarjamar kur'ani na kasar ya tarjama.

Harshen Wolof yana daya daga cikin muhimman harsuna a kasar ta Senegal wanda ake Magana da shi a matsayin ahrshe na biyu bayan harshen faransanci da yake a matsayin harshen kasa.

3578085


captcha