Wannan gasa da aka fara gudanarwa a jiya an kasa ta zuwa kashi biyu, da ya hada bangaren mata da kuma bangaren maza kuma ya hada da bangaren manya da kuma bangaren yara da matasa.
Aana gudanar da gasar ne a babban dakin karatu na cibiyar musulmi da ke birnin na Hamburg, kamar yadda kuma ake gudanar da ita a birnin Berlin da ma wasu kasashen turai da suka hada har da Danmark da kuma Sweden.
Masu alkalanci a bangaren mata sun hada da Yasmin Turkipour, Habibah Abdulali Hussaini, Zahra Musawi.
Bayan bangaren karatu, akwai bangaren tambayoyi na tafsiri a cikin surat Hud da kuma surat Yunus, daga tafsirin Ayatollah Naser Makarem Shirazi.