IQNA

Mace Musulma Mai Hijabi ta Farko A Gudun Marathon A Boston

20:47 - March 13, 2017
Lambar Labari: 3481310
Bangaren kasa da kasa, Rahaf Khatib musulma ce 'yar kasari Syria da zaune a kasar Amurka wadda za ta shiga wasan marathon a birnin Boston na Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin «aboutislam» cewa, wanann shi ne karon farko da wata mace musulma mai hijabi za ta shiga cikin wannan wasa mai tsohon tarihi a garin na Boston.

Khatib a zantarawrta da tashar NBC News ta bayyana cewa, babbar manufarta ita ce shiga cikin wannan wasa domin tabbatar wa masu tunanin cewa musulma mace da ke da lullubi ba za ta iya yin komai ba, domin su gane cewa suna yin kure.

Ta ci gaba da cewa, tun bayan da ta fara harkokin wasannai ba ta taba shiga cikin marathon na shekara-shekara da ake gudanarwa a birnin ba, amma a wannan karon ta yanke shawar cewa za ta shiga, kuma da yardar Allah za ta yi kwazo domin nema ma mata musulmi masu hijabi matsayinsu.

Dangane da irin matsalolin da suke fuskanta daga wasu masu tsukakken tunani kan muslunci kuwa, ta bayyana cewa ya kamata su san cewa har kullum 'yan adamtaka ita ce babban abin da ke banbance mutum da dabba.

Musulmi mutane ne kamar kowa, ba daga sama suka fado ba, suna yin duk abin da kowane mutum ke yi na aiki da hidimomin yau da kullum, kuma musulmi bas u da matsala da sauran mutane, suna zaune lafiya da kowa, domin kuwa shi muslunci tun farko yana a matsayin addinin zaman lafiya ne.

Khatib 'yar shekaru 33 da shiga kasar Amurka ne tun fiyeda shekaru ashirin da suka gabata, kuma a halin yanzu tana da yara guda uku.

3583634
captcha