IQNA

Mahukuntan Bahrain Sun Sake Dage Shari’ar Sheikh Isa Kasim

23:37 - March 14, 2017
Lambar Labari: 3481312
Bangaren kasa da kasa, kotun masarautar Bahrain ta sake dage zaman yanke hukunci a shari’ar da take gunarwa a kan babban malamin addini na kasar Sheikh Isa Kasim.

Tashar talabijin ta alalam ta bayar da rahoton cewa, a zaman da kotun da masarautar Bahrain ta gudanar domin yanke hukunci kan babban malamin addini na kasar Ayatollah Sheikh Isa Kasim, ta sake sake zaman har zuwa 7 ga watan Mayu na wannan shekara.

Tun daga makon da ya gabata masarautar Bahrain ta dauki kwararan matakai na tsaro a fadin kasar, domin murkuhse al’umma idan suka yi bore kan hukuncin da kotun masarautar kasar ke shirin yankewa akan babban malamin.

Wasu rahotanni sun ce kotun ta yi nufin yanke hukuncin korar Sheiikh Isa Kasim daga kasar Bahrain baki daya, bayan da masarautar kasar ta janye masa izinin zama dan kasar a ranar 20 ga watan Yunin 2016 da ta gabata.

Ayatollah Isa Kasim dai na daga cikin mutanen da suke yin kira zuwa ga adalci da daidaito a tsakanin al’ummar kasar Bahrain, tare da goyon bayan matakai na kawo gyara a tsarin tafiyar da mulki a kasar kasar, ba tare da tauye wa wani bangaren ‘yan kasa hakkokinsu saboda dalilai na bangaranci da banbancin mazhaba ba.

3584083

captcha