IQNA

Karuwar Kai Hare-Hare A Kan Masallatai A Kasar Amurka

22:52 - March 19, 2017
Lambar Labari: 3481328
Bangaren kasa da kasa, An samu karuwar kai hare-hare a kan masallatai da cibiyoyin musulmi a kasar Amurka a cikin wannan shekara ta 2017.

 Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shafin yada labarai na Islamic News na asar Amurka ya bayar da rahoton cewa, rahotanni da babbar cibiyar musulmin Amurka ta tattara dangane da hare-haren da aka kai wa masallatan musulmi a fadin kasar ya nuna cewa, daga watan Janairun farkon wannan shekara zuwa tsakiyar wannan wata na Maris, an kai hari a kan masallatai 32 a fadin kasar Amurka, daga ciki kuwa har da kone masallatai 11 kurmus.

Rahoton ya ce idan aka kwatanta da farmakin da masu kyamar musulmi suka kai a kan masallatai da cibiyoyin musulmi a kasar Amurka a cikin shekarar 2016, hare-haren watanni uku na farkon wanann shekara sun ninka har sau biyu, wanda hakan ke tababtar da karuwar tsanain nuna kiyayya da kyama ga msuulmia kasar Amurka, tun bayan da Donald Trump ya dare kan kujerar shugabancin kasar.

3585030

captcha