IQNA

Taron Nouruz Da Maulidin Fatima Zahra (SA) A Istanbul

23:42 - March 22, 2017
Lambar Labari: 3481335
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taro bukukuwan Nouruz da kuma na Maulidin Fatima Zahra a birnin Istanbul na kasar Turkiya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a daren jiya an gudanar da taron bukukuwan shigar sabuwar shekara shamsiyyah da kuma maulidin diyar manzon Allah Fatima (AS) a birnin Istanubl fadar mulkin Turkiya.

Taron dai ya samu halaratr jakadan kasar Iran a Turkiya, kamar yadda kuma da dama daga cikin Iraniyawa mazauana kasar ta Turkiya suka halarci wurin, gami da jama’ar gari da suke da shawa’ar halartar wannan taro.

An gabatar da jawabi da kuma wakoki na bege, da kuma masu dangantaka da shiga sabuwar shekara ta hijira shamsiyya a wurin.

A kowace shekara dai ana gudanar da bukukuwan shiga sabuwa shekara ta hijira shamsiyya akasashen Iran da kuma sauran kasashen da ske Magana da harshen farisanci, da kuma kasashen da suka hada al’adu iri daya.

3585446


captcha