IQNA

Jami’an Tsaron Bahrain Sun Kai Hare-Hare Kan Gidajen Jama’a

23:47 - March 22, 2017
Lambar Labari: 3481337
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron masarautar Bahrain sun kaddamar da farmakia kan gidajen jama’a a cikin yankin Satra bisa dalilai na bangaranci na banbancin mazhaba.

Kamfanin dillancin labaran Iqnanya bayar da rahoton cewa, a ci gaba da takura jama’a da kuma dnne musu hakkokinsu a matsayinsu na ‘yan kasa da masrautar mulkin kama karya ta Bahrain ke yi, a yau jami’an tsaron sun kai famaki kan gidajen jama’a a yankin satra.

Rahotanni sun tabbatar da cewa jami’an tsaron masarautar kasar wadanda mafi yawansu ba ‘yan kasar ta Bahrain ba ne, mutane ne da aka yi haya daga kasashen ketare domin gudanar da wannan aiki, sun shiga cin zarafin jama’a a yau kamar yadda suka saba.

A lokacin da suka isa yankin na Satra, sun shiga gidage kimanin 50 tare da keta alfamar ilayansu, da kuma kame mtane 40 da suka hada da kananan yara 8 suka yi awon gaba da su.

3585454

captcha