IQNA

Baje Kolin Tarjamar Kur'ani Mai Tsarki A Birnin London

21:16 - March 23, 2017
Lambar Labari: 3481338
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani baje kolin kwafin kur'anai da aka tarjama a cikin harsuna daban-daban a birnin London na kasar Birtaniya.

BKamfanin dillnacin labaran iqna ya nakalto daga shafin «Newham Recorder» cewa, an gudanar da wannan baje koli ne tare da nuna tarjamar kur'ani mai tsarki a cikin harsuna 50 na duniya

A yayin baje kolin daruruwan mutane wadanda ba musulmi sun halarci wurin, kuma sun duba wasu daga cikin ayoyin kur'ani da suke bukatar karin haske a kansu.

Daga cikin ayoyin da wasu suka yi tambaya a kansu har daayoyin jihadi a cikin kur'ani mai tsarki, inda aka basu gamsassshen bayani kan kan ma'anar jihadi a cikin kur'ani wadda kuma ita hakikanin ma'anarsa a cikin addinin muslunci.

Daga jawabin da aka bayar akwai cewa, shi jihadi yana nufin kokari a dukkanin fuskoki na ayyukan alkhairi, da suka hada da bautar Allah, da ayyukan jin kan bil adama, da taimakon marassa karfi da taimakon wanda aka zalunta, da ciyar da mabukaci, amma inda ya zo da ma'anar yaki, yana nufin kariyar kai ne ba yin shishigi a kan wasu ba, dalili kuwa shi ne, manzon Allah ya zauna tare da yahudawa da kiristoci a Madina kuma bait aba cutar da su ba.

Babbar manufar wannan baje kolin dai it ace kara kusanto da fahimtar mabiya addinai tare gane cwa muslunci ba addinin tashin hankali ba ne ko ta'addanci kamar yadda ake ta kokarin bayyana shi.

3585488
Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha