IQNA

Musulmin Birtaniya Sun Yi Allawadai Da Harin London

19:36 - March 24, 2017
Lambar Labari: 3481343
Bangaren kasa da kasa, musulmin kasar Birtaniya sun yi Allawadai da kakkausar murya dangane da harin ta’addancin da aka kai a birnin London.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, jaridar Guardian ta habarta cewa, babbar majalisar musulmin kasar Birtaniya ta fitar da bayani da ke yin Allawadai da kakkausar murya kan harin da aka kai kan jama’a abirnin London.

Harun Khan shi ne babban sakataren majalisar musulmin kasar ta Birtaniya ya bayyana cewa, wannan hari ba shi da wata alaka da addinin muslunci.

Haka nan kuma ya yi ga dukaknin musulmin kasar ta Birtaniya da kada su bari ayyukan ‘yan ta’adda su raba kawunansu, domin kuwa abin da yake faruwa yana babban tasiri wajen rarraba kan muuslmi.

A bangare guda kuma kwamitocin masallatai na cikin birnin London da ma wasu biranan kasar kasar sun fitar da bayanai daban-daban da ke yin Allawai da wannan mummunan aiki, tare da nisanta hakan da duk wata akida ta muslunci.

Kwamitin masallacin Birmingham ya fitar da wani bayani, bayan yin Allawadai da harin, ya kuma bayyana hakan a matsayin wani aiki na dabbanci, wanda dan adam da baya da addini ma ba zai yi hakan ba, balantana mai kiran kansa muslmi, wanda ya tababtar da cewa ‘yan ta’adda ba su da addini.

Sadiq Khan shi ne magajin garin birnin London, ya bayyana cewa abin ya faru ko shakka babu aiki ne na ta’addanci, kuma dole ne kowa ya yi Allawadai da hakan, amma kuma a lokaci guda hakan ba zaitaba zama dalili na kyamar musulmi ba, saboda wasu da ke kiran kansu musulmi sun aikata ta’addanci domin kashin kansu, domin kuwa ba suna wakiltar muslunci ba ne a lokacin da suka aikata ta’addanci.

3585523

captcha