IQNA

Malamin Kirista A Najeriya Ya Jaddada Wajabcin Tattaunawa Tsakanin Addinai

22:01 - March 25, 2017
Lambar Labari: 3481344
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin manyan malaman addinin kirista a Najeriya John Onaiyekan ya jadda wajabcin yattaunawa a tsakanin addinai a wani jawabinsa a jami'ar Notre Dame ta Indiana a Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin «catholicculture» cewa, babban malamin addinin kirista na Najeriya John Onaiyekan ya gabatar da jawabi ne a gaban taron da ake yin a duniya kan addinai a jami'ar ta Notre Dame a cikin jahar Indiana.

Ya ce babbar matsaar da ake fuskanta ita ce rashin fahimtar juna a tsakanin addinai, idan da za a mayar da tattaunawa ta zama a gaba a tsakanin mabiya addinai, to da an warware da dama daga cikin batutuwa da ake da rashin jituwa ko fahimta akansu.

Ya kara da cewa, ya kwashe tsawon shekaru fiye da 40 yana tattaunawa da bangarorin muslmi a Najeriya, a kan haka akwai kyakkyawar fahimtar juna tsakaninsa da musulmi, kuma haka lamarin yake tsakanin sauran mabiya addinain muslunci da kiristanci a Najeriya.

Dangane da batun ta'addanci kuwa, ya ce kungiyoyin ta'adda irin su Boko haram ba suna wakiltar musumi ba ne a ta'addancin da suke aikatawa, domin kuwa musulmin Najeriya basa kallon Boko Haram a wani bangare na muslunci, saboda haka rashin adalci ne a danganta ayyukan Boko haram da musulmin Najeriya.

3585602


captcha