IQNA

Paparoma Ya Gana Da Musulmi A Milan

23:43 - March 26, 2017
Lambar Labari: 3481347
Bangaren kasa da kasa, jagoran mabiya addinin kirista na darikar Katolika Paparoma Fransis ya gana da wasu muulmi a cikin birnin Milan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Paparoma Francis ya ziyarci gidan Mika’il Abdulkarim wani dan asalin kasar Morocco mazaunin birnin Milan.

A lokacin da yake ziyara a gidan wadannan musulmi, Paparoma Francis ya bayyana cewa, ko shakka babu addinin mulsnci da addinin kiristanci suna da tushe guda daya ne, saboda haka mabiya addinain guda biyu ‘yan uwan juna ne.

Shi ma a nasa abangaren Abdulkarim ya bayyana jin dadinsa matuka dangane da wannan ziyara da paparoma Francis ya kawo a gidansa, tare da bayyana hakana matsayin wani babban lamari na tarihi a gare shi.

Wasu daga ciki mazauna ginin da Abdulkarim yake wadanda mabiya addinin kirista ne, sun yi amfani da wannan damar domin ganawa da Paparoma, tare da gabatar da wasu bukatunsu a gare shi.

Daga nan kuma ya wuce zuwa wani gidan kaso, inda ya gana da fursunoni, tare da jin korafe-korafen da suke da su, haka nan kuma ya zauna tare da su domin cin abincin rana.

3585726

captcha