IQNA

Babban Malamin Palastine:

Dole Shugabannin Larabawa Su Bayar Da Muhimmancin Kan Palastine

21:49 - March 27, 2017
Lambar Labari: 3481350
Bangaren kasa da kasa, Babban malami mai bayar da fatwa a birnin Quds da sauran yankunan Palastinu Sheikh Muhammad Hussain ya kirayi shugabannin larabawa da cewa, ya zama wajibi a kansu da su bayar da muhimamnci a kan batun Palastinu da Quds a zaman da za su gudanar a kasar Jordan.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, 

A cikin jawabi da ya fitar a yau, babban malamin na Palastinu ya bayyana cewa, babban abin da al'ummar Palastinu da sauran musulmi da larabawa suke tsammani daga shugabannin larabawa a zaman da za su gudanar a birnin Amman na Jordan shi ne, su dauki kwararan matakai na fuskantar matakan cin zalun da kisan kiyashin da Isra'ila take yi wa Palastinawa a kullum rana ta Allah, haka nan kuma musulmi na jiran su ga matakan da za a dauka a wannan taro domin fuskantar barazanar da Isra'ila take yi na rusa wurare masu tsarki a addinin muslunci, musamman a birnin Quds.

Malamin ya kara da cewa, matsaloli da dama da musulmi suka shiga suna suna da alaka da makircin Isra'ila ne, domin kuwa  ahalin yanzu musulmi da larabawa sun manta da Quds sun koma suna yakar junasu, yayin da Isra'ila kuma take ci gaba da cin karenta babu babbaka a kan al'ummar muuslmi na palastinu da kuma wurare masu tsarki na musulmi, da suka hada da alkiblar musulmi ta faro wato masallacin Quds.

A ranar Laraba mai zuwa ce shugabannin kasashen larabawa za su gudanar da zamansu a karo na 28 a birnin Amman na kasar Jordan.

3585858


captcha