Taron wanda ya hada mata zalla, ya dauki hankulan manema labarai na ciki da wajen kasar ta Birtaniya, musamamn ganin yadda daruruwan mata musulmi da suke sanye da lullubi na muslunci suka shiga cikin taron, tare da bayyana alhininsu kan abin da ya faru.
Bayan faruwar lamarin wasu masu kyamar msuulunci sun yi amfani da wannan damar domin kara ruruta wutar kyamar musulmi a kasar, amma magajin garin birnin London da kuma shugaban jam'iyyar Labour ta kasar Birtaniya, sun ja hankulan al'ummar kasar da su san cewa abin da ya faru ba zai taba zama dalili na cutar da musulmi ko nuna musu tsangwama ba, domin kuwa kusan dukkanin musulmin Birtaniya ba su goyon bayan hakan, kuma suna yin Allawadai da abin da ya faru.