IQNA

Wasu Masu Kyamar Muslunci Sun Kai Hari Kan Masallaci A Amurka

22:20 - March 27, 2017
Lambar Labari: 3481352
Bangaren kasa da kasa, wasu masu kyamar addinin muslunci sun kai hari kan wani masallaci a birnin Colorado inda suka karya tagogin masallacin.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, shafin yada labarai na  matashi wanda shekarunsa ke tsakanin 20 zuwa 30 ya kai farmakia cikin dare a kan wani masallaci na musulmi, inda ya karya tagogi tare da jefa kwafin littafin Injila.

Wannan dai shi ne karon farko da aka kai wani farmaki makamancin haka akan wannan masallaci wanda yake hade da cibiyar muslunci, inda musulmi suke salla kuma suke gudanar da tarukansu na addini.

Bayan sanar da jami'an tsaro a bin ya faru, sun dauki mataki gudanar da bincike domin gano wanda yake da ahhnu a cikin lamari domin daukar mataki na doka a kansa.

Musulmi a kasar Amurka dai suna fuskantar matsalolin tsangwama da kyama sakamakon ayyukan ta'addanci da wasu amsu dauke da akidar wahabiyanci suke aikatawa da sunan muslunci a kasar da ma sauran kasashen turai.

Yayin da musulmi ke kokrin wayar wa mutanen wadannan kasashen da kai a kan cewa, 'yan ta'addan wahabiyya takfiriyya suna kasha musulmi fiye da yadda suke kasha sauran mutane wadanda ba musulmi, domin a kullum rana sai sun kai hare-haren bama-bamaia cikin kasashen msuulmi a yankin gabas ta tsakiya.

3585822


captcha