IQNA

An Fara Taron Dubi Kan Manhajar Makarantun Musulmi A Turai

23:47 - March 28, 2017
Lambar Labari: 3481353
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani zaman taro domin yin dubi a kan manhajar karatu na makarantun musulmia cikin nahiyar turai tare da halartar wakilai daga Faransa, Italiya, Spain da kuma Holland.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa na fara gudanar da zaman taron ne karkashin kulawar babbar cibiyar kula da ilimi da al’adun musulunci ta dniya ISESCO a birnin Granada na kasar Spain.

Bayanin ya ci gaba da cewa, babbar manufar taron wanda mambobin kwamitin kula da harkokin ilimi na kasashen turai ne suke gudanar da shi, ita ce kara samar da ingantaccen tsari wajen koyar da addinbi a makaranttun musulmi da ke turai.

Tun bayan da aka fara samun matsaloli na kyamar msuulmi a cikin kasashen turai sakamakon bullar kungiyoyin ‘yan ta’adda masu dauki da akidar kafirta musulmi, aka fara fuskantar matsaloli a makarantun musulmi a wasu kasashen turai.

Wasu daga cikin masana musulmi sun yi kofari a kan cewa, akwai gyara a cikin wasu manhajojin koyarwa makarantun msuulmi, domin kuwa daga nan ake samun masu tsatsauran ra’ayi da suke cusa akidar ta’addanci da sunan musluncia cikin zukatan matasan musulmi.

Wasu daga cikin makarantun msuulmi a kasashen turai sun taka rawa wajen samar da ‘yan ta’adda da suka tafi jihadi a wasu kasashe, wanda hakan ya nuna wajabcin samar da kyakyawan tsari da kuma sanya ido kana bin da ake koyarwa a cikin irin wadannan makarantu.

3585936

captcha