IQNA

An Kafa Dokar Hana Raba Kur’ani A Wuraren Jama’a A Kasar Austria

23:41 - March 30, 2017
Lambar Labari: 3481360
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Austria ta afa dokar hana raba kur’ani da kuma saka nikabi a wuraren hada-hadar jama’a a fadin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alraya.co cewa, gwamnatin kasar Austria ta kara fadada dokoki da suka shafi ‘yan gudun hijira a kasar musamman musulmi daga cikinsu.

Bayanin ya ce wannan doka ta shafi hana saka nikabi ko duk wani abu da zai rufe fuska a cikin wurare na hada-hadar jama’a a kasar, kamar yadda kuma aka hana raba kwafin kur’ani a cikin jama’a, kuma wanda ya saba wannan doka zai biya tara ta yuro 150.

Wannan doka na daga cikin sabbin dokoki masu tsauri da gwamnatin kasar ta Austria ta kafa bisa hujjar shawo kan matsalolin da ake fuskanta sakamakon yawaitar ‘yan gudun hijira a kasar.

Baya ga hakan kuma gwamnatin Austria ta sanya halartar sammun horo na shekara guda ga ‘yan gudun hijira ya zama wajibi, dominsanin harshe da kuma al’adu da dokokin kasar, wanda kuma rashin halartar wannan horo ga ‘yan gudun hijira, zai jawo tara a kansu da kuma yanke musu tallafin da gwamnatin kasar ke ba su.

3586136

captcha