Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na Qaf cewa, ana shirin fara gudanar da wata gasar kur'ani mai tsarki a garin Basara a lokacin tunawa da zagayowar haihuwar Imam Ali (AS).
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa za ta kebanci yara mata zalla da adadinsu zai kai kimanin 250 wadanda za su fito daga birane daban-daban na kasar.
Daya daga cikin wadanda suka shirya wannan gasar ya bayyana cewa, za su yi amfani da wanann damar wajen kara karfafa gwiwar matasa da kuma 'yan mata wajen mayar da hankali a kan lamarin kur'ani mai tsarki.
Baya ga gasar kur'ani, za a baje kolin kayayykin tunawa da wadanda suka yi shahada domin kare kasar a wajen yaki da 'yan ta'adda.