IQNA

Wani Dalibi Musulmi Ya Gayyaci Firayi Ministan Canada Zuwa Masallaci

23:46 - April 06, 2017
Lambar Labari: 3481382
Bangaren kasa da kasa, wani yarondalibin makaranta musulmi a garin Saint John da ke Canada ya gayyaci firayi ministan kasar zuwa masallaci.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CBC News cewa, Abdullah Shahwan wani dalili ne muuslmi da shekarunsa bas u wuce 12 ba da haihuwa.

Wannan dalibi ya aike da wata wasika zwa ga firayi ministan kasar Canada yana gayyatarsa zuwa masallaci, domin ya ganewa idanunsa abin da musulmi suke yi a cikin masallaci.

Ya ce ya dauki wannan mataki ganin irin yadda kyamar musulunci ke ta karuwa a tsakanin al’ummar Canada, inda a kwanakin baya ma wani ya shiga da bindiga ya kasha musulmia cikin masallaci suna salla, ba tare da sun aikata wani laifi ba, sai domin kawai yana kin jininsu.

Wannan lamari a cewarsa, yana bukatar mahukntan kasar su bayyana ma jama’a matsayrsu kana bin da yake faruwa, hakan kuwa zai fi muhimmanci ne idsan suka zo inda musulmi suke domin ganewa kansu abin musulmi suke yi, ibada suke yi ba fada da wani ba, ko ta’adda kamar yadda ake zarginsu.

Daga karshe ya ce ya yi farin ciki matuka a lokacin da ya ga firayi ministan kasar ta Canada ya halarci janazar musulmin da aka kashe a masalaci a kwanakin baya.

3587179


captcha