IQNA

Taron Kur’ani A Lokacin Haihuwar Imam Ali (AS) A India

23:41 - April 07, 2017
Lambar Labari: 3481384
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da karatun kur’ani a lokacin taron maulidin Imam Ali (AS) wanda ya yi daidai da 13 ga rajab.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na imamhussain.org cewa, za a gudanar da wannan taron ne tare da halartar dubban masoya iyalan gidan manzo.

Wannan taro dai zai gudana ne bisa daukar nauyin hubbarorin Imam Hussain (As) da kuma Abbas (A) kuma taron zai gudana n kamar yadda aka saba a kowae shekara.

Baya ga karatun kur’ani da makaranta da mahardata suke gudanarwa a wajen taron, haka nan kuma malamai sukan gabatar da jawabai da kuma tunatar da mutane a kan matsayin ailan gidan manzo.

Sheikh Ali Alfatlawi wakilin hubbaren mai tsarki na daga cikin wadanda za su gabatar da jawabai a wurin, kamar yadda kuma za a gabatar da wakokin yabo da bege ga manzon Allah da kuma iyalan gidansa tsarkaka.

3587487


captcha