IQNA

Kafar Sadarwa Domin Yaki Da Tsattsauran Ra’ayi A Gabashin Afirka

23:21 - April 13, 2017
Lambar Labari: 3481403
Bangaren kasa da kasa, an bullo da wata sabuwar hanyar sadarwa ta yanar gizo da nufin yaki da tsattsauran ra’ayin addini a kasar Kenya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wannan hanayar za ta mayar da hankali ne wajen gdanar da ayyukanta a yanar gizo, domin shirin nata ya zama na kasa da kasa.

Babbar manufar kirkiro da wannan hanya dai ita ce, wayar da kan musulmi musamman matasa daga cikinsu, kan hakikanin koyarwqar musulunci, da kuma yadda yake yin kira zuwa ga kyawawan dabiu da kauce ma shiga hakkokin wasu.

Ganin kasar Kenya ba kasar musulmi ba ce, amma tana da musulmi wadanda yawansu abin la’akari nea kasar, da kuma yadda wasu kasashe suka yi tasiri a cikin kasar ta Kenya wadanda suke da yawan musulmi.

A lokutan baya-bayan nan kasar ta Kenya ta yi fama da ‘yan ta’adda da suke shigowa kasar, kamar yadda wasu daga cikinsu ma ‘yan kasar ne, kuma abin ban takaici shi ne dukkanin masu aikata ayyukan ta’addanci a cikin kasar ta Kenya muslmi ne.

Musulmi musamman matasa daga cikiinsu suna shiga kungiyoyin ta’addanci da sunan addini ne bisa jahilci, inda gwamnatocin wasu kasashen larabawa da suke da hannu wajen kafa kungiyoyi masu tsatsauran ra’ayi suna kafirta musulmi suna kira’ansu ‘yan bidi’a da saransu, su ne kan gaba wajen haifar da wannan masifa a cikin kasashen duniya.

3589363



captcha