IQNA

Amnesty Int. Ta Bukaci Mahukuntan Bahrain Da Su Saki Sheikh Ali Salman

20:23 - April 14, 2017
Lambar Labari: 3481404
Bangaren kasa da kasa, kungiyar Amnesty Int. ta bukaci mahukuntan kasar Bahrain da su gaggauta sakin Sheikh Ali Salman ba tare da wani sharadi ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga Tashar pressTV ta bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da Amnesty Int. ta fitar dangane da danne hakkokin bil adama da masarautar Bahrain ke yi, ta bukaci masarautar da ta gaggauta sakin Sheikh Ali Salman, shugaban jam’iyyar Alwifaq jam’iyyar mafi girma akasar ta Bahrain.

Bayanin na Amnesty Int. ya ce an kame Sheikh Ali Salman da kuma tsare shi ne saboda dalilai na siyasa, sakamkon kiran da yake yi ga masarautar kasar kan a bayar da dama ga al’ummar kasar su zabi wadanda suke bukata su wakilce a majalisa.

A ranar 28 ga watan Disamban 2014 ve dai jami’an masarautar Bahrain suka kame sheikh Ali Salman, bayan yanke masa hukuncin daurin shekaru 9 bisa zarginsa da yin kalamai na sukar tsarin masarautar kasar na mulkin mulukiya, daga bisani an sassauta hukuncin zuwa shekaru hudu.

Tun a ranar 14 ga watan fabrairun shekara ta 2011 ne dai al'ummar kasar Bahrain suka fara gudanar jerin gwano na lumana domin neman a kare hakkokinsu an 'yan kasa, tare da ba su damar kada kuri'a domin zaben majalisar dokoki da za ta wakilce su, amma mahukunatna maimakon amsa kiran jama'a sai suka dauko sojojin hana suka ci gaba da kisan jama'a.

3589452

captcha