Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakal;to daga shafin yanar gizo na al-Hayat cewa, wannan taro an yi masa taken taskar musulunci a Afirka.
Taron bude baje kolin ya samu halartar shugabannin kasashen Mauritania, Mali, Burkina Faso da kuma Francios Hollande na kasar Faransa mai masafkin baki.
A lokcin bude taro, shugaban kasar Farasa ya gabatar da jawabi, inda yake bayyana arewacin nahiyar Afirka a matsayin yanki mai dogon tarihi, kamar yadda kuma ko bayan zuwan muslunci wannn yanki ya taka rawa wajen yada shi zuwa sauran yankuna naAfirka.
Daga cikina bubuwan da aka baje kolinsu a wurin, akwai littafai da wasu kayan tarihi kimanin guda 300, wasu daga cikinsu suna komawa ne zuwa shekaru dubu da dari uku da suka gabata.
Daga cikin wadannan litfafai da kayan tarihin muslunci da aka baje a wannan wuri, akwai wadanda aka kawo daga birnin Tinbuktu, birnin tarihin ilimi a arewacin nahiyar Afirka, wadanda ya samar da manyan malamai da ake alfahari da sua duniyar yau a nahiyar Afirka.