Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, karamin ofishin jakadancin kasar Iran a kasar Philipines ya sanar da fara gudanar da taron ranar tunawa da aiko ma'aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.
Babbar manufar gudanar da wannan taro dai ita ce tunawa da ranar aiko manzon Allah, wanda ya zo wa dan adam da sako tsira daga halaka da kuma fita daga duhun kafirci da jahilci
Manzon Allah (SAW) ya kasance mutum na musamman a cikin larabawa, wanda dukkanin al'ummar da ke tare da shi ta yi masa shedar gaskiya da rikon amana da karamci da kuma girmama jama'a, wadada suka grime shi da ma wadanda ya girma.
Allah madaukain sarki ya aiko da sako zuwa ga bil adama, wanda ya zama sanadin shiririyar jama'a da dama a lokacinsa, mafi yawan wadanda suka muslunta tare da manzon Allah a Makka sun sun musulunta ne sakamakon kyawawan dabiunsa, kamar yadda da dama daga cikin wadanda suka muslunta aMadiana bayan hijira sun karbi muslunci ne sakamakon kyawawan dabiu da suka gani tare da manzon Allah, wadanda addinin ke koyar da dan adam.
3592826