IQNA

Hubbaren Alawi ya Karbi Bakuncin Miliyoyin Jama’a A Daren Mab’as

23:23 - April 25, 2017
Lambar Labari: 3481437
Bangaren kasa da kasa, a daren jiya hubbaren alawi mai tsarki ya karbbi bakuncin miliyoyin jama’a domin tunawa da mab’as.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labarai na hubbaren alawi daga birnin najaf cewa, an gudanar da taruka na tunawa da ranar aiko manzon Allah (SAW) a hubbaren Imam Ali (AS) da ke birnin Najaf Ashraf.

Bayanin ya ci gaba da cewa, an gudanar da wanann taro ne tare da daukar matakan tsaro da kuma bayar da kariya ta musamman ga mahalarta taron da suka fito daga sassa na kasar Iraki da ma wasu kasashen duniya.

Hubbaren Imam li (AS) ya saba karbar bakuncin tarukan addini da suka hada da tarukan tunawa da haihuwa ko shahadar iyalan gidan manzon Allah, kamar yadda wannan rana mai albakrka tana daga cikin muhimman ranaku na muslunci da ake gudanar da taruka a kansu a wannan wuri mai tsarki.

Sayyid Nazzar Habl Matins hi ne shugaban cibiyar da ke kula da wannan hubbare mai tsarki, ya kasance daga cikin mahalrta taron na jiya, wanda yake a matsayin rana ta addini.

3593136

captcha