Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shafin yada labarai na Gaza Now ya bayar da rahoton cewa a cikin wasikar, Marwar Barguthi ya bayyana cewa; sun shiga yajin cin abinci a gidajen kason Isra'ila, domin neman a kyautata yanayin rayuwarsu, da kuma kawo karshen takura da cin zarafin da Isra'ila ke yi wa dubban Palastinawa da take tsare da su a gidan kaso.
Ya ce suna kira ga 'yan majalisun dokoki na kasashen duniya, da hakan ya hada da majalisar kungiyar tarayyar turai, kan su bi kadun halin da Palastinawa suke ciki a gidajen kason Isra'ila.
Yanzu haka dai fursunonin Palastinawa 1500 ne karkashin jagorancin marwan Barguthi suka shiga yajin cin abinci a gidajen kason kason Isra'ila, domin tilasta mahukuntan Isra'ila da su saurari bukatunsu, musamman halin kunci da suke ciki a gidajen kaso.