IQNA

Mahalarta Taron Gasar Kur’ani Sun Gana Da Jagora

23:57 - April 27, 2017
Lambar Labari: 3481443
Bangaren siyasa, mahalrta gasar kur’ani mai tsarki da aka gudanar a birnin Tehran sun gana da jagoran juyin juya halin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ofishin jagora cewa, a yau jagora Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya gana da mahalrta gasar kur’ani karo na 34 da aka gudanar a birnin Tehran.

Bayanin ya ce baya ga dukkanin wadanda suka halarci wanann gasa, wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin kasar Iran sun halarci wannan ganawa da jagoran juyin juya halin, da suka hada da Syyid Ridha Salehi Amiri ministan kula da harkokin al’adun muslunci, da ma sauran jami’ai.

Wannan gasa dai ta samu halartar makaranta da mahrdata da kuma malamai da masana kan lamarin kur’ani mai tsarki daga kasashe 83, kamar yadda kuma adadin bakin da suka halarci gasar daga kasashen ketare ya kai mutane 400 daga kasashen duniya daban-daban.

A farkon bude taron ganawar da jagora, fitaccen makarancin kur’ani mai tsarki daga kasar ta Iran Ahmad Abul Kasimi ya gabatar da karatu, inda ya karanta ayoyin kur’ani mai tsarki, kamar yadda kuma wasu daga cikin mahalartan suka gabatar da nasu karatun

Haka nan kuma wasu daga cikin malamai da makaranta sun gabatar jawabi na godiya ga jamhuriyar muslunci a kan daukar nauyin wanna gasa da ta yi, gami da hidimar da ta yi a kan wannan lamari, domin daukaka sha’anin kur’ani mai tsarki da kuma girmama shi.

A wannan karon dai an kasa gasar ne zuwa kashi hudu, da hakan ya hada da bangaren na farko na makaranta da mahardata kamar yadda aka saba, sai kuma bangaren nakassau, da kuma bangaren mata, sai kuma bangaren daliban jami’oi da suka so daga kasashe daban-daban.

Daga karshe jagoran juyin juya halin muslunci ya gabatar da nasa jawabin, inda ya bayyana haduwa domin kur’ani mai tsarki da cewa hakika wannan babban lamari ne na bautar ubangiji, domin kuwa kur’ani mai tsarki shi ne littafin shiriya da Allah ya aiko manzonsa da shi.

Bin wannan littafi shi ne tsira ga dukkanin talikai, domin kuwa a cikinsa ne shiriyar ubangiji take, wadda manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi bayaninta dalla-dalla ga dukkanin bil adama, a cikin kalaminsa da kuma a dukkanin ayyukansa.

Jagoran ya yi fatan alkhairi da kuma dacewa da falala da albarka da ke cikin alkur’ani mai tsarki ga dukkanin mahalrta wannan gasa, da ma wadanda dukkanin sauran al’ummar musulmi baki daya.

3593700


captcha