IQNA

An Raba Kwafin Kur'ani Dubu 40 A Kasar Gambia

21:57 - April 28, 2017
Lambar Labari: 3481445
Bangaren kasa da kasa, an raba kwafin kur'ani mai tsarki guda dubu 40 a kasar Gambia da nufin kara yada koyarwar kur'ani a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin thepoint.gm cewa, cibiyar kula da harkokin al'adu ta kasar Gambia ce ta jagorancu aiwatar da wannan shiri, tare da taimakon cibiyar jin kai ta kasar Qatar.

Wannan cibiya dai ta kan gudanar da ayyuka irin wannan a cikin kasar ta Gambia tare da hadin gwiwa da ma'aikatar yada al'adun muslunci ta kasar, daga cikin ayyukan kuwa har da gina masallatai da makarantu da sauransu.

Babbar manufar raba wadannan kwafin kur'anai dai ita ce wadata kur'anai a hannun jama'a, ta yadda za su samu damar karanta wanann littafi mai tsarki tare da samun ladar da ke tattare da hakan.

Baya ga hakan kuma wannan cibiya tana taimaka maiyalai marassa karfi a kasar, da kayan abinci da sauran abubuwan bukatar rayuwa.

Kasar Gambia dai tana a yammacin nahiyar Afirka ne, kuma kashi 90 cikin dari na mutanen kasar musulmi ne, sauran kashi 10 kuma sun hada da kiristoci na Katolika da protestant da sauran addinai na gargajiya na Afirka.

3593697

captcha