IQNA

Kenya Zata Karfafa Harkokin Abincin Halal A Kasarta

23:41 - April 30, 2017
Lambar Labari: 3481452
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar ta sanar da cewa tana shirin kara karfafa harkokin samar da abincin halal a cikin kasarta.

Shugabankaramin ofishin jakadancin kasar Iran a Kenya a zantawarsa kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kasar ta Kenya na shirin kara karfafa harkokin da suka shafi samar da kayayyakin halal a cikin kasar.

Ministan kula da harkokin yawon bude na kasar Kenya ne ya sanar da hakan a lokacin da yake ganawa da jami'an huldar diflomasiyya na kasar Iran a kasar ta Kenya.

Ministan ya ce wanann tsari zai kasance ne isa kaidoji na addinin muslunci wajen samar da irin wadannan kayayyaki, bisa la'akari da cewa kasar Kenya kasa ce mai karbar bakia kowane lokaci daga kasashen duniya daban-daban.

Ya ce daga cikin bakin da suke zuwa Kenya akwai musulmi daga kasashen larabawa da sauransu, wadanda sukan bukaci abincin halal tsawon lokacin da zamansu a kasar, kuma rashin samun wadataccen kayayyakin halal a kasar zai kawo nakasu matuka wajen kasa gamsar da baki musulmi.

A kan haka ya jaddada cewa kasashen Kenya da Iran za su yi aiki kafada da kafada wajen samar da irin wadannan kayayyaki a cikin kasar, duk kuwa da cewa tuni an riga an fara shirin, kuma an fara ganin amfaninsa matuka.

3594523
captcha