IQNA

Za A Fara Koyar Da Wani Darasi Na Muslunci Da Kiristanci A Masar

23:43 - April 30, 2017
Lambar Labari: 3481453
Bangaren kasa da kasa, za a fara koyar da wani darasi na kyawawan dabi'un addinan kiristanci da musluncia kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo nan a Almuwatin cewa, Ikram Lam'i shugaban kwamitin nazarin Injila na a kasar Masar ya bayyana cewa, za a samar da wani darasi wanda za a rika koyar da kyawawan dabiu a cikin addinan muslunci da kiristanci a makarantun firamare da sakandare na kasar Masar.

Ya ce babbar manufar wannan shiri ita ce kara samar da fahimta da zaman lafiya atsakanin mabiya addinan biyu a kasar, kuma darasin zai kunshi ayoyi ne daga kur'ani da kuma Injila, wadanda suke magana a kan kyawawan dabiu da zaman lafiya, da taimakon juna da makamantan hakan.

Haka nan kuma a cewarsa shirin zai kasance ne tare da hadin gwiwa a tsakanin manyan majami'u da kuma cibiyar azhar, ta yadda ba za a fitar da wani abu ba sai dukkanin bangarorin biyu sun amince da shi.

3594549
captcha