IQNA

An Fara Gasar Kur'ani Ta 'Yan Jami'a A Lebanon

22:40 - May 02, 2017
Lambar Labari: 3481458
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar kur'ani ta 'yan jami'a karo na bakwai a kasar Lebanon mai take gasar Sayyid Abbas Musawi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na Qaf cewa, a jiya an fara gudanar da gasar kur'ani ta Sayyid Abbas Musawi ta 'yan jami'a a kasar Lebanon.

Wannan gasa dai wadda ake gudanarwa a karo na bakwai ta kebanci daliban jami'a ne kawai, inda ake gudanar da gasar a dukkanin bangarori, da suka hada har da bangaren tajwidi.

Bangaren kula da ayyukan yada al'adu na gwagwarmayar muslunci a Lebanon ne ke daukar nauyin wannan gasa, da nufin kara karfafa gwiwar matasa a kan lamarin kur'ani mai tsarki, da kuma yin riko da koyarwarsa.

Sayyid Abbas Musawi dai daya ne daga cikin malaman addini a kasar Lebanon, ya yi yaki tare da Palastinawa 'yan gudun hijira a kan Isra'ila, amma daga bisani ya koma kasar Iraki domin ci gaba da karatu, sai ya fuskanci matsala daga mahukuntan kama karya na gwamnatin ba'asiyya a Iraki, a lokacin da ya dawo Lebanon ya ayar da Himma wajen karfafa Hizbullah domin yaki da Isra'ila, ya tasirantu da marigayi Ayatollah Bakir sadr da kuma Imam Khomenei (RA).

Ya zo Iran a cikin shekara ta 1979, an kuma zabe shi a matsayin babban sakataren kungiyar Hizbullaha shekara ta 1991, a ranar 16 ga watan Fabrairun 1992 ne ya yi shahada.

3595215
captcha